IQNA

Kiran A Dauki Mataki Kan Wariyar Da Ake Nuna Ma Musulmi A Amurka

23:43 - October 12, 2017
Lambar Labari: 3481994
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da harkokin musulmi ta jahar Michigan a kasar Amurka ta bukaci da a dauki kwararan matakai na kare musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai detroinews cewa, a jiya cibiyar kula da harkokin musulmi ta jahar Michigan a kasar Amurka ta bukaci da a dauki kwararan matakai na kare musulmi musaman a bangaror na sufuri.

Bayanin ya ci gaba da cewa babban dalilin da ya jw hakan shi ne irin yadda jami’an tsaron gwamnatin Arka ske cin zarafin matafiya musulmi a filin jiragen sama, na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a jahar ta Michigan.

Yamar musulmi da nuna musu karan tsana yana karuwa cikin sauri a Amurka, tun bayan da sabuwar gwamnati ta karbi mulki, gwamnatin da tazo da sunan kymar musulmi da kin jinin baki.

Yanzu haka musulmi mazauna kasar ta Amurka suna kokawa kan yadda cin zarafinsu ya zama a hkumance ne, sabanin lokutan baya, inda wasu masu kyamar musulmi ne kawai suke cin zarafinsu, inda yanzu jami’an tsaron gwamnatin kasar ne tare da izinin gwamnatin suke cin zarafin musulmi.

3652054


captcha