IQNA

Martanin 14 Ga Fabrairu Kan hana Sallar Juma’a A Bahrain

20:45 - October 13, 2017
Lambar Labari: 3481997
Bangaren kasa da kasa, gungun 14 ga watan fabrairu ya mayar da martani dangane da matakin da masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta dauka na hana babbar sallar Juma’a akasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Mana Post cewa, gungun matasa na sha hudu ga watan fabrairu ya mayar da martani dangane da matakin da masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta dauka na hana babbar sallar Juma’a a kasar da ake gudanarwa a masallacin Imam Sadeq (AS) a yankin Deraz karkashin jagorancin Ayatollah sheikh Isa Qasem.

Matakin da masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta dauka na hana sallar juma’a mafi girma a kasar na a matsayin danne hakkokin al’ummar kasar musamman mabiya mazhabar ahlul bait wadanda su ne suka fi yawa.

Masautar ta saka daruruwan jami’an tsaroa cikin kaya sarki dauke da bindigogi da motoci masu sulke, wadanda suke sanya ido tare da hana gudanar da sallar juma’a amasallacin Imam Sadeq (AS) da ke a yankin na Deraz.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gaba masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta kaddamar da farmaki da dukkanin makamanta akan gidan babban malamin addini na kasar tare da kasha wasu daga cikin mabiyansa, yayin da shi kuma suka sanya cikin daurin talala.

3652202


captcha