IQNA

An Bukaci Azhar Ta Sake Yin Nazari Kan Tarjamar Kur’ani A Masar

23:43 - October 14, 2017
Lambar Labari: 3481999
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Hasanain wani mai bincike kan lamurran muslunci a kasar Masar ya bayyana cewa, tarjamar kur’ani da ake sayarwa a kasuwa tana dauke da kurakurai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na ahlmisrnews ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Hasanain wani mai bincike kan lamurran muslunci a kasar Masar ya bayyana cewa, tarjamar kur’ani da ake sayarwa a kasuwa tana dauke da kurakurai da dama.

Ya ce wajibi ne kan cibiyar Azhar da ta dauki kwararan matakai na hana yaduwar irin wadannan kwafin kur’ani da ke yawo a hannun jama’a da aka tarjama acikin harshen turanci, domin kuwa suna bayar da wata ma’ana wadda ba ita ce ake nufi ba.

Ya kara da cewa tun farko bai kamata azhar ta bari a fara yada wadannan kwafin kur’anai ba har sai ta tabbatar da an tantance su yadda ya kamata domin kaucewa fadawa cikin juya ma’anar kur’ani.

Daga karshe ya yi kira da a tattara wadannan kur’anai har an kammala tantance su baki daya kafin a bayar da dama sayar da su a kasuwa.

3652350


captcha