IQNA

Jiragen yakin Isra’ila sun kaddamar da munanan hare-hare a yankin Zirin Gaza

19:26 - August 28, 2020
Lambar Labari: 3485127
Tehran (IQNA) Jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da munanan hare-hare a yankin Zirin gaza.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, tun  da kimanin karfe biyu na daren jiya Alhamis ne jiragen yakin gwamnatin yahudawan Isra’ila suka fara kaddamar da wasu munanan hare-hare a cikin yankin zirin Gaza har zuwa asubahin yau.

Rahoton ya ce jiragen yakin na yahudawan Isra’ila sun kai hare-haren nea  akn wasu wurare na ‘yan gwagwarmaya masu fafutuka na kungiyar Hamas da ma wasu kungiyoyin na dabana.

Sai dai a lokacin da jiragen yakin gwamnatin yahudawan Isra’ila ke kai hare-haren, kungiyar Hamas da wasu kungiyoyin gwagwarmaya sun mayar da martani makamai masu linzami a kan matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna.

Hamas ta gargadi Isra’ila da cewa, idan ta ci gaba da kai wadannan hare-hare a kan yankin Gaza, to kuwa ta saurari martani mafi muni a kanta.

 

 

 

 

3919547

 

 

captcha