IQNA

A karon farko an kada taken Isra'ila a cikin kasar Saudiyya

15:39 - July 12, 2023
Lambar Labari: 3489459
Riyadh (IQNA) A karon farko a tarihin kasar Saudiyya, a lokacin gudanar harkokin masu alaka da gasar cin kofin duniya ta hukumar kwallon kafa ta duniya, an buga taken Isra'ila a birnin Riyadh.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masu amfani da shafukan sada zumunta na Isra’ila sun yada faifan bidiyo da ke nuna yadda aka daga tutar wannan gwamnati da kuma yadda ake gudanar da taken haramtacciyar kasar Isra'ila a babban birnin kasar Saudiyya.

Avi Nir Feldklein, jakadan gwamnatin Sahayoniya a Norway da Iceland, ya rubuta a cikin wani sakon twitter game da hakan: Pragmatism ita ce kadai hanyar samun zaman lafiya da sulhu.

Wannan dai shi ne karo na farko a tarihi da ake kada taken Isra'ila a wani biki a hukumance a kasar Saudiyya. Tun da farko kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa tawagar kwallon kafa ta Isra'ila ta shiga kasar Saudiyya dauke da fasfo din kasar ta UAE domin halartar wannan zagayen wasannin da Riyadh ta dauki nauyi.

Yayin da masana harkokin siyasa ba su yi hasashen kyakkyawan tsari na kulla alaka tsakanin Riyadh da Tel Aviv ba, majiyoyin labaran yahudawan sahyoniya sun kara kaimi kan ziyarar tawagar wasanni ta yahudawan Sahayoniya zuwa kasar Saudiyya ta kasar UAE.

A halin da ake ciki kuma, duk da kokarin diflomasiyyar Amurka, har yanzu Saudiyya ba ta son bayyana matsayinta kan kulla alaka a hukumance da Isra'ila.

4154543

 

captcha