IQNA

Fatah Ta Bukaci Falastinawa Da Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Mamaye Yankunansu

23:50 - June 22, 2020
Lambar Labari: 3484915
Tehran (IQNA) Fatah ta bukaci falasdinawa su fi zanga-zangar don nuna rashin amincewarsu da shirin mamaye yankin gabar yamma da kogin Jordan.

Kungiyar Fatah ta falasdinawa wace Mahmud Abbas ya ke jagoranta ta bukaci falasdinawa su fi zanga-zangar ranar “Fushi” don nuna rashin amincewarsu da shirin haramtacciyar kasar Isra’ila  na mamaye yankin gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran SAMA ya nakalto kakakin kungiyar Usama Kawamisi yana fadar haka, ya kuma kara da cewa a halin yanzu falasdinawa sun shiga wata sabuwar marhala a gwagwarmayan da suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kawamisi ya ce wa falasdinwan, “Mu tashi mu kare kasarmu, mu kuma daga murya, da cewa “bama son mamaya, allawadai da kaskanci, kuma Qudus ne babban birnin Falasdinu.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3906104

A cikin watan Yuli mai kamawa ne gwamnatin HKI ta kuduri anniyar kwace iko da yankin yamma da kogin Jordan na kasar Falasadinu da ta mamaye.

A wani labarin kuma gwamnatin kasar Jordan ta bada sanarwan cewa, idan HKI ta mamaye yankin yamma da kogin Jordan, to kuwa za ta warware dukkan alkawula da ta kulla da HK a baya.

captcha