IQNA

Amnesty Int. Ta Bukaci Saudiyya da Ta Saki Wani Babban Kusa Na Kungiyar Hamas

22:48 - August 13, 2020
Lambar Labari: 3485081
Tehran (IQNA) kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bukaci mahukuntan Saudiyya da su saki Muhammad Khidri.

Kamfanin dillancin labaran Falastinu ya bayar da rahoton cewa, Amnesty International ta bukaci mahukuntan Saudiyya da su saki Muhammad Khidri daya daga cikin amnyan jagororin kungiyar Hamas da ta suke tsare da shi.

Bayanin ya ce fiye ad shekara guda kenan Saudiyya tana tsare ad Dr. Muhammad Khidri, daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas, kuma wakilin kungiyar a kasar Saudiyya.

Bayan kama shi kungiyoyin kare hakkin bil adam na kasashen turai sun bukaci Saudiyya da ta gaggauta sakinsa, amma Saudiyya ta ce ba wata babbar matsala ce ba, zai amsa wasu tambayoyi ne kawai zaa sake shi, amma fiye da shekara guda kenan ba a sake shi ba.

Mahkuntan masarautar Al saud sun kame Muhammad Khidri ne tare da dansa Hani, wadanda babu cikakken bayani kan halin da suke ciki, ko suna raye ko kuma ba su a  raye.

3916368

 

captcha