IQNA

Trump Ya Sanar Da Cimma Yarjejeniyar Kulla Alaka Tsakanin UAE Da Isra'ila

22:52 - August 13, 2020
Lambar Labari: 3485082
Tehran (IQNA) Donald Trump ya sanar da cimma wata yarjejeniya ta kulla huladr diflomatsiyya tsakanin Isra’ila da kuma kasar UAE.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da cimma wata yarjejeniya ta kulla hular diflomatsiyya mai  tsakanin Isra’ila da kuma kasar Hadaddiyar daular Larabawa.

Wanann na zuwa a wani bayyani da ya yi wa manema labarai ranar Alhamis, Trump, ya danganta yarjejeniyar da gagarumar nasara tsakanin manyan kawaye biyu, wacce a cewarsa zata kawo karshen zaman dar-dar a gabas ta tsakiya baki daya.

Haka nan kuma yarjejeniyar a cewar Trump, ta tanadi da dakatar da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falasdinawa.

Ya kara da cewa nan gaba kadan za a kara samun wasu kasashen Musulmin da zasu kulla yarjejeniyar diflomasiya da Israila ba da jimawa ba.

Wasu bayanai sun ce an cimma yarjejeniyar da aka kwashe tsawon lokaci ana yi biyo bayan wata tattaunawa da bangarorin uku da suka hada Shugaban na Amurka, da fira ministan Isra’ila, da kuma yarima mai jiran gado na UAE.

Bayan fitar da wannan sanarwa kungiyar Hamas dake rike da karfin iko a yankin Gaza ta sanar da yin watsi da yarjejeniyar, yayin da Fira ministan Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana ranar a matsayin ranar tarihi a cewarsa.

Kasashen larabawan yankin tekun Fasha sun jima suna da alaka ta boye tsakaninsu da Isra'ila, amma a halin yanzu ya fara fitowa a fili.

 

3916445

 

captcha