IQNA

Zarif Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Zagayowar Ranakun Samun Nasara A Kan Sahyuniyawa

22:38 - August 14, 2020
Lambar Labari: 3485083
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Iran ya isar da sakon taya murna dangane da zagayowar cikar shekaru 14 da samun nasarar al'ummar Lebanon a kan yahudawan Isra'ila.

A cikin wani sako da ya rubuta zuwa ga takwaransa na Lebanon da kuma baban sakataren kungiyar Hizbullah, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, ya taya murna dangane da zagayowar cikar shekaru 14 da samun nasarar al'ummar Lebanon a kan yahudawan Isra'ila da korarta daga Lebanon.

A yau ne Zarif ya isa kasar Lebanon domin ganawa da manyan jami'an gwamnatin kasar da kuma jajanta musu kan abin da ya faru a Beirut.

 

3916471

 

captcha