IQNA

Siyasar Wasan Kwaikwayo Ta Amurka A Afghanistan

20:28 - June 28, 2021
Lambar Labari: 3486057
Tehran (IQNA) a ci gaba da dauki ba dadin da ake yi tsakanin dakarun gwamnatin Afghanistan mayakan Taliban sun sake kwace wasu yankuna a arewacin kasar.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, mayakan kungiyar Taliban a kasar Afghanistan suna ci gaba da kara tsananta hare-harensu a yankunan arewacin kasar, inda ake ci gaba da artabu tsakaninsu da dakarun gwamnatin kasar.

Rahoton ya ce, mayakan na kungiyar Taliban suna yin amfani da manyan makamai a gumurzun, wanda hakan yasa ala tilas dakarun gwamnati suka ja da baya a wasu yankunan, inda su kuma mayakan na Taliban suka mamaye su.

Daga cikin garuruwan da Taliban ta mamaye daga jiya zuwa, akwai garin Andokhi, sai kuma Khan Chahar Bagh, wadanda duk suna cikin gundumar Faryab da ke arewacin kasar ta Afghanistan.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta sanar da cewa, tana shirin kwashe sauran ragowar sojojinta da ke kasar Afghanistan, wadanda yawansu ya kai sojoji 2,500.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa, zai janye sojin Amurka daga kasar ta Afghanistan ne daga nan zuwa ranar 11 ga watan Satumban wannan shekara da muke ciki.

Da dama daga cikin masu bin diddigin lamarin dai sun yi imanin cewa, bayan kwashe tsawon shekaru goma da Amurka ta kaddamar da harin kasar Afghanistan tare da mamaye kasar, da sunan kawo karshen kungiyar Taliban, bisa zargin kungiyar da bai wa Ben Laden mafaka, ya zuwa yanzu babu abin da Amurka ta haifarwa kasar in banda rashin tsaro, da kuma jefa rayuwar mutane cikin mawuyacin hali.

Siyasar Wasan Kwaikwayo Ta Amurka A Afghanistan

Daga abubuwa masu sanya shakku kan lamarin na Amurka, har da kasancewar kungiyar Taliban ta kara karfi a cikin wadannan shekaru goma fiye da owane lokaci a  baya, maimakon murkushe kungiyar ko kawo karsheta baki daya.

Irin takun da Joe Biden yake yi a cikin siyasarsa, wanna yasa wasu suke ganin cewa har yanzu ba ta canja zane ba a cikin lamurra da dama na siyasar tsohon shugaban Amurka Donald Trump, inda suke ganin hatta batun janyewar sojojin Amurka daga Afghansitan akwai wata makarkashiyar ta daban da aka shirya a cikin wannan lamari, wanda tabbas zai cutar da al’ummar Afghanistan.

Siyasar Wasan Kwaikwayo Ta Amurka A Afghanistan

 

3980348

 

captcha