IQNA

Shugabannin Hamas Da Jihadul Islami Sun Tattauna Da Ibrahim Ra'isi

19:05 - July 14, 2021
Lambar Labari: 3486106
Tehran (IQNA) Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran za ta ci gaba da goyon bayan al-ummar Falasdinu

A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, zababben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran za ta ci gaba da goyon bayan alummar Falasdinu, a gwagwarmyan da suke yi da yahudawan Sahyoniyya wadanda suka mamaye kasarsu.

Ra’isi ya bayyana hakan ne a zantawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban kungiyar Hamas a bangaren siyasa Isam’ila Haniyya da kuma babban sakaren kungiyar Jihadul Islami Ziyad Nakhala a jiya Talata.

Sayyid Ibrahim Ra’isi ya kara ta ya al-ummar Falasdinu nasarar da suka samu a fafatawa ta karshe da yahudawan Sahyoniyya na kwanaki sha daya.

Sannan a nashi bangaren Isama’ila Haniyya ya taya Sayyid Ra’isi murnar zabensa a matsayin shugaban kasar Iran, ya kuma yi masa fatan alkhairi a ayyukasa.

Hakama Ziyad Nakhala ya taya zabebben shugaban murnar zabensa da kuma fatan All..ya bashi damar sauke nauyin da aka dora masa, sannan ya kara godiya ga Iran kan tallafin da take bawa al-ummar Falasdinu a gwagwamayar da suke yi da yahudawan sahyuniya.

 

3983972

 

 

 

 

captcha