IQNA

Kotun Tarayyar Turai Ta Halasta Korar Mata Masu Sanye da Hijabi A Wuraren Ayyuka

20:11 - July 15, 2021
Lambar Labari: 3486107
Tehran (IQNA) kotun kungiyar tarayyar turai ta yanke hukunci kan halascin korar mata musulmi da suke sanye da hijabi daga wuraren ayyukansu.

A rahoton da ta tashar Alajazeera ta bayar, a zaman da kotun tarayyar turai ta gudanar kan karar da aka shigar kan korar wasu mata biyu musulmi daga wuraren ayyukansu a kasar Jamus, kotun ta yanke hukunci kan cewa, wadanda suke da wuraren ayyuka ko kasuwanci, za su iya daukar duk hukuncin da suka ga ya dace kan hakan.

Bayanin kotun ya ce, masu wurare za su iya duba maslaharsu, idan saka lullubi ko wani nau'in tufafi zai iya jawo wa kasuwancinsu ko ayyukansu matsala, to za su iya tilasta masu saka wanann nau'in tufafin su cire su, ko kuam su dauki matakin da suka ga ya dace, da hakan ya hada har da kora, kuma yin hakan bai saba wa 'yancin bayyana akida ta addini ba.

Wannan hukunci na kotun tarayyar turai ya zo bayan shigar da kara da aka yi, kan korar musulmi biyu mata daga wuraren ayyukansu a kasar Jamus saboda saka lullubi irin na addinin muslunci.

Daya daga cikin matan musulmi tana aiki ne a wata makarantar kananan yara wadda ba ta gwamnati ba a matsayin malama a birnin Hamburg na kasar Jamus, inda aka umarce ta da ta cire hijabi, bayan da taki amincewa da hakan aka sallame ta daga ikinta, kamar yadda irin hakan ya faru da wata msuulmar, wadda take aiki a amtsayin ma'aji a wani dakin sayar da magani.

 

3984341

 

 

 

 

 

 

 

captcha