IQNA

Dakarun Hashd Alshaabi Sun Fatattaki 'Yan Ta'addan Daesh A Iraki

20:42 - July 15, 2021
Lambar Labari: 3486108
Tehran (IQNA) dakarun Hashd Alshaabi sun fatattaki mayakan 'yan ta'adda na kungiyar Daesh a kan iyakokin Iraki da Syria

Dakarun gamayyar kungiyoyin sa kai na al’ummar Iraki masu tabbatar da tsaro a kasar, da aka fi sani da Hashd Alshaabi sun sami nasara dakile wani yunkurin shigowar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a garin Jurfun-Nasr daga arewacin lardin Babuil na kasar.

Wasu majiyoyi a cikin rundunar ta tabbatar da cewa, a lokacin da kammala aikin korar mayakan na daesh tare da hana su shigowa cikin Iraki daga Syria, motar da ke dauke da dakarun ta taka wata nakiya wadda ‘yan ta’addan suka dana, wanda kuma ya yi sanadiyyar yin shahadar daya daga cikin dakarun.

Kafin haka dai dakarun Hashdu ne suke gadin dogayen sandunan wayoyin wutan lantarki a kasar wadanda kungiyar ta Daesh ta dade ta na lalata su. Kamar yadda ta yi a lardunan Diala da kuma Ninawa. A halin yanzu dai dakarun Hasdu su ne ginshikin tsaron kasar Iraki, sannan masu tallafawa sojojin da sauran Jami’an tsaron kasar ta Iraki.

 

3984267

 

 

captcha