IQNA

Jagoran Juyi Na Iran Ya Isar Da Sako Ga Mahajjatan Bana

21:59 - July 19, 2021
Lambar Labari: 3486120
Tehran (IQNA) jagoran juyin juya halin mulunci na Iran ya isa da sako ga mahajjan bana, wanda ya mayar da hankali kan tunatarwa dangane da muhimman abubuwan da suke a matsayin kalu bale ga al'umma.

Kamar kowace shekara,a  shekarar bana ma jagoran juyin juya halin mulunci na Iran Ayatollah Sayyid ali Khamenei ya isa da sako ga mahajjan bana, wanda ya mayar da hankali kan tunatarwa dangane da muhimman abubuwan da suke a matsayin kalu bale ga al'ummar musulmi.

Ga wani bangare daga matanin jawabin nasa:

Bayan godiya ga Allah, Ubangijin talikai, da neman tsira da aminci ga ma’aikinsa Muhammad (SAW), jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, ya bayyana cewa wannan ita ce shekara ta biyu ta rashin jin dadi da musulmi basu samu damar gudanar da aikin hajji ba, sakamakon annobar korona, ko wata killa manufofin wadanda suka mamaye massallacin Ka’aba mai tsarki sun hana masu imani ganin al’kibilarsu.

Jagoran ya kara da cewa, Wannan jarabawar ta yi kama da sauran abubuwan da suka gabata a tarihin al'ummar musulmi, wanda zai iya haifar da kyakkyawar makoma.

Abin da ke da muhimmanci shi ne cewa ko ba’a gudanar da aikin Hajji ba, ya kasance a raye a cikin zukata da rayukan Musulmai.

Irin jawabin da Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ke fitarwa wadanda ke girgiza kasashe masu girman kai na duniya, shi ne zai iya zamo makami na kawo karshen tsoma bakin Amurka da kuma kasashe ‘yan takala.

‘’Da juriya ne kawai za’a iya kawo karshen tsoma bakin Amurka a cikin harkokin kasashen musulmi’’ 

A ci gaba da sakon nasa, Ayatullah Khamenei ya tabo babbar matsalr da take addabar duniyar musulmi wadda ita ce irin tsoma baki cikin lamurran duniyar musulmi da Amurka da kawayenta suke yi don haka ya ce gwagwarmaya da tsayin daka su ne mabudin kawo karshen wannan tsoma baki na Amurka da ‘yan amshin shatan nata cikin lamurran duniyar musulmi.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa Amurka da ‘yan amshin shatanta suna tsananin damuwa da kalmar tsayin daka da gwagwarmaya don haka suke nuna kiyayya da adawa da masu gwagwarmayar.

A wani bangare na sakon nasa Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da kokarin da makiya suke yi ta hanyar farfaganda wajen kashe gwuiwa da kuma zubar da mutumcin ‘yan gwagwarmayar ta hanya nuna su a matsayin yaran Iran wanda ya ce ko da wasa lamarin ba haka ya ke ba.

Yayin da ya ke magana kan abin da ke faruwa a kasar Afghanistan kuwa, Ayatullah Khamenei ya kirayi al’ummar kasar da su yi taka tsantsan kada su fada tarkon da Amurka ta dana musu ta hanyar ficewar da ta yi daga kasar bayan mamaya ta shekaru ashirin.

Har ila yau kuma Jagoran yayi ishara da alkawarin Allah na taimakawa da kuma ba da nasara ga wadanda suka tsaya bisa tafarkinsa yana mai ishara da irin gwagwarmaya da tsayin dakan da al’ummomin kasashen Falastinu, Yemen da Iraki suka yi a matsayin alamun da suke tabbatar da gaskiyar wannan alkawari na Ubangiji.

Shi dai wannan sako na Jagoran kamar yadda aka saba a kan karanto shi ne a can kasar Saudiyyan yayin da ake hawan Arafat wato ranar 9 ga watan Zulhajji inda ake karanto sakon ga maniyyatan sannan daga baya kuma a isar da shi zuwa ga sauran al’ummar musulmi na duniya.

A cikin sakon dai Jagoran ya kan tabo manyan matsalolin da suka addabi al’ummar musulmi da kuma gabatar da hanyoyin da za a magance su.

 

 

3985039

 

 

captcha