IQNA

Falastinawa Fiye Da Dubu 100 Ne Suka Sallar Idi A masallacin Aqsa A Yau Talata

22:00 - July 20, 2021
Lambar Labari: 3486124
Tehran (IQNA) Falastinawa fiye da dubu 100 ne suka yi sallar Idin layya a yau a masallacin Aqsa.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a yau Falastinawa fiye da dubu 100 ne suka yi sallar Idin layya a masallacin Aqsa, duk kuwa da irin tsauraran matakan da jami'an tsaron yahudawan Isra'ila suka dauka.

Sheikh Muhammad Hussain babban mai bayar da fatawa na birnin Quds ne ya jagoranci sallar, inda ya yi huduba dangane da abubuwa da suke da muhimamnci ga musulmi su mayar da hankali a  kansu, tare da komawa zuwa ga Allah.

Sannan kuma ya bayyana cewa, dole ne mutane su rika kiyaye ka'idoji na kiwon lafiya, musamman wannan lokaci da cutar corona take kara tsananta a wasu sassa na naduniya.

 

 

3985377

 

captcha