IQNA

UAE Ta Dauki Kwararan Matakai Na Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi A Makarantun Kur’ani

21:58 - May 12, 2015
Lambar Labari: 3294190
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a kasar UAE sun dauki kwararan matakai na shiga kafar wando daya da koyar da tsatsauran ra’ayin addini a makarantun koyar da kur’ani mai tsarki da ke kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Imarat Al-youm cewa, shugaban kwamitin kula da harkokin koyarwa a bangaren kur’ani a ma’aikatar kula da harkokin addi ta kasar ya bayyana cewa sun dauki kwararan matakai na shiga kafar wando daya da koyar da tsatsauran ra’ayin addini a makarantun koyar da kur’ani mai tsarki tare da sanya ido sosai a kansu.

Ahmad Ubaid Mansur wanda shi ne babban jami’I mai kula da harkokin da suka shafi koyarwa a bnagren lamurran kur’ani a maiakatar kula da harkokin addini ta kasar hadaddiyar daular larabawa ya bayyana cewa, sun dauki wadannan matakan da nufin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a halin yanzua  kasashen larabawa na ta’addanci da sunan addini.

Ya ci gaba da cewa daga cikin muhimamn abubuwan da suke yia  shirin nasu har da daukar matakai na yin gyaran fuska dangane da tsarin manhajar koyarwa a cikin wadannan makarantu tare da sanya ido kan dukaknin abin da ake koyarwa, domin tabbatar da cewa an yi amfani da tsarin nasu.

Dangane da yadda ake aiwatar da shi kuma ya ce ya zuwa yanzu ba su da wata matsala ko fargaba dangane da lamarin, amma kuma duk da haka za a su ci gaba da bin tsarin sau da kafa domin tababtar da cewa ya yi tasiri.

3287619

Abubuwan Da Ya Shafa: uae
captcha