Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hamrain News cewa, Hamad Almazrui wani marubucin kasar hadaddiyar daular larabawa kuma na hannun damar yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, ya soki lamirin malaman wahabiyawa masu bata sunan muslunci.
Shi dai wannan marubuci a kasar hadaddiyar daular larabawa ya yi wanann rubutu ne na kakakusar suka dangane da yadda malaman wahabiyawa suke wuce gona da iri wajen gaba da addini bayan kai garin Saudiyyah.
Almazrui y ace malaman wahabiya da malaman yahudawa duk makiya addinin muslunci ne, kuma duk abin daya suke yi domin rusa addinin muslunci, inda ya bayar da misali da wasu fitattun malaman wahabiyawa kamar Al-uraifi da kuma Al’audah, wadanda suka shahara wajen cutar da addini.
Ya ce irin wadannan malamai sun shahara a duniyar musulmi wajen bata sunan muslunci, tare da bakanta shia fuskar duniya, da suka da su Al’Uraifi, Al’audah, Alkarni, Alqardawi, Alsuwaidan, Aludha da sauransu, wadanda ya ce babu wanda ya kais u gaba da muslunci.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Almazrui yake sukar malaman wahabiyawa ba.
3341812