IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Shaikha Hind Bin Maktum A UAE

23:27 - February 09, 2018
Lambar Labari: 3482379
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta Shikha Hind Bint Maktum a kasar hadaddiyar daular larabawa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alkhalij cewa, a gobe ne za a fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta Shikha Hind Bint Maktum a kasar hadaddiyar daular larabawa a karo na goma sha tara.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa tana daga cikin muhimman tarukan gasar kur’ani da ake gudanarwa  akasar tun kimanin shekaru goma sha tara da suka gabata, kuma gasar tana samun karbuwa da bunkasa daga bangaren cikin gida da kuma kasashen ketare.

Kamar dai yadda aka saba ana gudanar da gasar ne a bangarori na harda da kuma karatu na tilawa, wanda hakan zai bayar da dama makaranta da kuma masu harda su shiga dukkanin bangaren da suke bukata.

Bayan kammala gasar dai a kan bayar da kyautuka na baki daya ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, yayin da kuma ake bayar da wasu kyautukan na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

A bana a bangaren maza akwai mahalarta 66, sai kuma bangaren 78, sai kuma masu nakasa 19 da za su shiga gasar.

3690036

 

 

 

captcha