IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai Da Batunci Ga Fitattun Mutane A Muslunci Da Wasu Suka Yi A Lebanon

23:56 - June 08, 2020
Lambar Labari: 3484875
Tehran (IQNA) babbar cibiyar musulunci ta Azahar da ke Masar ta yi Allawadai da kalaman batunci a kan wasu manyan mutane a addini da wasu suka yi a Lebanon.

Jaridar Yaum Sabi ta kasar Masa ta bayar da rahoton cewa, a yau babbar cibiyar musulunci ta Azahar da ke Masar ta yi Allawadai da kalaman batunci a kan wasu manyan mutane a addini da wasu suka yi a Lebanon tare da bayyana hakan da cewa ba abu ne da za a aminta da shi ba.

A ranar Lahadi ne wasu suka fito da sunan nuna adawa da gwamnati a Lebanon daga nan kuma sai suka shiga yin kalaman batunci a kan wasu fitattun mutane da ake girmamawa a cikin addini.

Tun bayan faruwar lamarin kungiyar hizbullah ta yi Allawadai da kakkausar murya kan hakan, tare da bayyana irin wadannan ayyukan da cewa basa wakiltar wani addini balantan addinin musulunci wanda shi ne ke koyar da dan adam kyawawan halaye da dabi’u na gari.

Azhar ta bukaci gwamnatin Lebanon da malaman addini da su dauki kwararan matakai a kan duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan aiki na ashha.

Daga bisani jami’an tsaron sun sanar da cewa sun kame wasu larabawa da suka shigo kasar da nufin aiwatar da ajandidi na wasu kasashe da nufin kawo hargitsi a kasar.

 

 

3903630

 

captcha