IQNA

Hadadddiyar Daular Larabawa Na Karfafa Kawance da Isra’ila

22:28 - October 20, 2020
Lambar Labari: 3485292
Tehran (IQNA) gwamnatin Hadadddiyar Daular Larabawa na kara karfafa kawancenta da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta zamanto kasar Larabawa ta farko da ‘yan kasar ta ba sa bukatar takardar izinin shiga wajen shigaba haramtacciyar kasar Isra’ila biyo bayan yarjejeniyar da ta cimma da ‘Isra’ila a wannan bangaren.

Hakan kuwa yana cikin wata sanarwa ce da firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yayi jim kadan bayan isar wata tawaga ta jami’an UAE din da suka isa Tel Aviv inda ya ce a yau sun kafa tarihin da zai ci gaba da wanzuwa da kuma amfanar zuriya masu zuwa.

A yau Talata ne wani jirgin Hadaddiyar Daular Larabawan na Etihad Airways dauke da wasu jami’an UAE da na Amurka da suke rufa musu baya ya sauka a filin jirgin sama na Ben Gurion Airport da ke birnin Tel Aviv.

A yayin da yake maraba da jami’an UAE din, Netanyahu ya ce bangarori biyun sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi guda hudu a jiya Litinin, daga cikinsu kuwa har da yarjejeniyar dage takardar Visar a tsakaninsu.

Wannan dai yana zuwa bayan yarjejeniyar kulla alaka ta dipmasiyya da aka cimma tsakanin UAE da Isra’ilan a kwanakin baya lamarin da har ya zuwa yanzu take fuskantar tofin Allah tsine daga bangarori daban-daban na duniyar musulmi da na larabawa.

 

3930029

 

captcha