IQNA

Malamai A Aljeriya Sun Bukaci Gwamnati Da Ta Sake Bude Makarantun Kur’ani

23:14 - December 18, 2020
Lambar Labari: 3485469
Tehran (IQNA) malaman musulmi a kasar Aljeriya sun bukaci a bude makarantun kurani a kasar sakamakon rufe su da aka yi saboda yaduwar cutar corona.

Shafin jaridar Al-shuruq ya bayar da rahoton cewa, a yau malaman musulmi a kasar Aljeriya sun fitar da wani bayani, wanda a cikinsa suka bukaci gwamnati ta bayar da damar sake bude makarantun kurani a kasar sakamakon rufe su da aka yi saboda yaduwar cutar corona.

Bayanin ya ce, bisa la’akari da cewa an dauki tsawon lokaci makarantun kur’ani suna rufe, duk da cewa akwai na karatu ta hanyar yanar gizo, amma ko kadan ba zai kai halartar makaranta ba.

Haka nan kuma bayanin malaman na kasar Aljeriya ya kara da cewa, babbar matsalar da ake kokawa a kanta ita ce cutar corona, wanda kuma za  aiya yin sari na kariya daga kamuwa daga cutar a dukkanin makarantu, tsakanin shugabannin makarantun da kuma hukumomin kiwon lafiya.

Kasar Aljeriya na daga cikin kasashen arewacin nahiyar Afirka da ake yin amfani da tsohon tsarin karatun allo da aka gada daruruwan shekaru da suka gabata a kasar.

3941757

 

 

 

 

captcha