IQNA

Shugaba Ra'isi: Amurka Ce Ummul Haba'isin Gurgunta Yarjejeniyar Nukiliya Tare Da Iran

21:45 - August 22, 2021
Lambar Labari: 3486228
Tehran (IQNA) Shugaba Ibrahim Ra’isi, na Iran ya jadadda wajabcin ganin kasar Japan ta sake wa Iran kudadenta da take rike da.

Shugaban wanda ke bayyana hakan yayin wata ganawa da ministan harkokin wajen kasar Japan dake ziyara a kasar ta Iran, ya bayyana cewa jinkirin da ake samu wajen sakarwa Iran da kudadenta da bankunan Japan suka rike ba shi da wani dalili.

Hakan kuma Iran, ba ta da wata matsala game da hanyoyin da za’a bi wajen tattaunawa game da wannan batun.

A daya bangaren kuma shugaban kasar ta Iran, ya godewa kasra ta Japan, game da tallafin jin kan da ta baiwa Iran a yaki da annobar cutar korona, tare da fatan bangarorin zasu ci gaba da aiki tare domin murkushe wannan annobar ta covid-19 a kasashen biyu dama duniya baki daya.

Lokacin da yake bayyani ga ministan harkokin wajen kasar ta Japan game da batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, shugaba Ebrahim Ra’isi, ya ce tun cen fil azal Iran tana mutunta yarjejeniyar, Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa tare da kakabawa Iran jerin takukumai.

 

3992354

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tattaunawa tallafi bangarori
captcha