IQNA

Wasu Bama-Bamai Sun Tashi A Babban Masallacin Birnin Kabul Na Kasar Afganistan A Yau

15:47 - April 06, 2022
Lambar Labari: 3487131
Tehran (IQNA) Wani harin bam da aka kai a masallacin Khashti da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan a yau , ya yi sanadin mutuwa da kuma jikkatar mutane.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na tashar Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, an samu fashewar wani abu da ake sa ran bam ne a masallacin gadar Khashti, masallaci mafi girma a birnin Kabul, a lokacin sallar azahar a yau Laraba, bam din ya tashi ne a gaban masallacin.

Ahmad Shah, wanda ya shaida lamarin, ya shaidawa tashar Afghan News cewa fashewar ta faru ne a lokacin da mutane ke cikin sallar azahar.

Ya kara da cewa, an kai harin ne a kusa da wurin da jami’an ‘yan sanda ke binciken masu wucewa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla biyu, Wasu majiyoyi kuma sun ce akalla mutane shida ne suka jikkata a lamarin.

Kakakin 'yan sandan Kabul Khalid Zadran ya ce an kama wani da ake zargi da hannu a lamarin.

Bidiyon da ke ƙasa yana nuna ɗan lokaci bayan fashewar ta'addanci a Masallacin.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4047286

 

captcha