IQNA

Shahararren Mawaki A Amurka Ty Dolla Sign Ya Musulunta

16:38 - November 28, 2023
Lambar Labari: 3490221
Dubai (IQNA) Bayan ya musulunta, shahararren mawakin nan dan kasar Amurka Ty Dolla Sign ya yi sallarsa ta farko a wani masallaci inda ya samu kyautar Alkur'ani. An watsa faifan bidiyo a lokacin yake a wani masallaci, wanda masu amfani da shafukan intanet suka yi maraba da shi.

A wani rahoto da shafin Lialina ya watsa, shahararren mawakin nan na Amurka Ty Dolla Sign, ya yi sallarsa ta farko a masallacin bayan ya musulunta.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yada wani faifan bidiyo na mawakin rap yana sallar farko a wani masallaci.

A cikin wannan bidiyon, an ga Ty Dola Sign  kusa da wani da ke koya masa yadda ake sallah. Bayan an idar da sallah, Dola Sign ya yi musafaha da wannan mutumi, shi kuma  ya baiwa Sign kur'ani.

Wannan faifan bidiyo ya yadu a shafukan sada zumunta kuma mutane da yawa sun danna alamar suna son bidiyon tare da yi masa fatan samun nasara a sabon addininsa.

A karon farko, Rashid Belhasa, shahararren marubucin shafin yanar gizo na Masarautar, ya bayyana ta hanyar buga faifan bidiyo cewa wasu shahararrun mawakan rap a duniya biyu sun musulunta. Ya kuma bayyana musuluntar NLE Choppa da Dola Sign.

Balhasa ya sanar da cewa Chopa ya musulunta ne mako guda da ya gabata a daya daga cikin manyan masallatan Hadaddiyar Daular Larabawa. Da yake bayyana bidiyon Chopa yana salla, ya rubuta cewa: “Ina alfahari da kai, dan uwana Chopa, wanda ya yi imani da Allah daya, Alhamdulillah”. Ina rokon Allah Ya shiryar da ku zuwa ga hanya madaidaiciya”.

Chopa ya rubuta a shafinsa na Instagram: “Na yi imani cewa Allah yana tare da mu a duk inda Na yi imani da sallah. Na yi imani da Allah, da addininsa ina neman gafararsa, zan dukufa da ayyukan ibada”.

 

 

 

4184558

 

captcha